'Yan Nageria sun cika garaje da gajen hakuri - Shugaba Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari ya ce 'yan Nigeria suna da gajen hakuri na son rayuwar su ta inganta cikin gaggawa fiye da karfi da arzikin da kasar ke da shi.
Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke jawabi kan bukin sabuwar shekarar 2018.
Ya ce ya jima yana bibiyar al'amuran da ke gudana musamman muhawara da wasu ke yi na batun sake fasalin kasar, kuma idan aka hada ra'ayoyin al'umma wuri guda, ya yi amannar matsalolin kasar sun fi karkata ne kan hanyar da ake bi ba tsarin da ake kai ba.
KU KARANTA: Anyi zazzaga a gidan sojin sama na Najeriya
Legit.ng ta samu dai haka zalika yace babu wata doka ko wani al'amari na dan Adam da ya cika dari bisa dari, a don haka duk wani tsari da aka bullo da shi wajibi ne a rika inganta shi lokaci zuwa lokaci domin ya da ce da ci gaba ta fuskar siyasa da tattalin arzikin kasa.
Shugaba Buhari ya ce idan aka hada ra'ayoyin al'umma wuri guda, ya yi amannar matsalolin mu sun fi karkata ne kan hanyar da ake bi ba tsarin da ake kai ba.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng