Ana bata-kashi a wani gida: Bayan da mijinta ya saiwa mai-aikin gidan babbar waya mai dankaren tsada

Ana bata-kashi a wani gida: Bayan da mijinta ya saiwa mai-aikin gidan babbar waya mai dankaren tsada

- Mai aikin budurwa ce 'yar shekara 17

- Uwar gidan ta koka ne a shafukan sada zumunta

- Mai gidan ya saya wa yarinyar wayar N100,000 a matsayin murnar Kirsimeti

Ana bata-kashi a wani gida: Bayan da mijinta ya saiwa mai-aikin gidan babbar waya mai dankaren tsada
Ana bata-kashi a wani gida: Bayan da mijinta ya saiwa mai-aikin gidan babbar waya mai dankaren tsada

Wata mata ta koka kan irin alakar da ke tsakanin mijinta da har ya iya sayawa mai aikin gidanta dankareriyar waya har ta N100,000 da sunan kyautar bikin kirsimeti.

Matar wadda ta sakaya sunanta, ta ce kuma ta lura N3,000 da ta kashe wajen yiwa yarinyar gyaran gashi, ba ita ce a kan yarinyar ba, akalla kan yarinyar yaci N10,000.

Ta nemi shawara kuma wai wurin dattijuwar mahaifiyarta wadda ke zama a gidan, tsohuwa tace bata ga wani abin zargi ba.

DUBA WANNAN: Kasar Iran zata dauki mataki kan masu zanga-zangar lumana

A cewar matar dai, wadda ba'a bayyana sunanta ba, ta ce "mai-aiki na tana da kyau da cikar halitta, kamar su qugu da kutiri, da ma kirji, kuma ina zarginta da biye wa yaran makwabta..."

Ta kuma kara da cewa, kokarin ta na ta kori yarinyar yaci tura domin maigidan ya haramta a kori yarinyar, inda yace marainiya ce.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng