Hatsarin mota yayi sanadiyar mutuwar mutane 15 a jihar Jigawa

Hatsarin mota yayi sanadiyar mutuwar mutane 15 a jihar Jigawa

- Mumunar hatsari mota yayi sanadiyar mutuwar mutane 15 a Jigawa

- Hatsarin ya auke ne yayi da karamar mota kirar Golf ta hade da Tipan diban yashi

- Shugaban karamar hukumar Gwiwa ya ce duka fasinjoji da suka mutu mazauna garin Gwiwa ne

Akalla mutane 15 suka rasa rayukan su ta sanadiyar hatsarin mota da ya auku a yammacin ranar Asabar yayin da wata Tippan dibar yanshi ta hade da karamar mota a jihar Jigawa.

Hatsarin ya auku ne a Garin Ciroma, wani kauye dake kusa da karamar hukumar Gagarawa a jihar Jigawa da misalin karfe 9.30 na yamma.

Hatsarin ya auku ne yayin da Wata karamar mota kirar Volkswagen Gulf 3 mai lamba AA 664 DRA ta debo fasinjoji 15 kuma cike da kaya daga karamar hukumar Gwaram zuwa karamar hukumar Gwiwa ta hade Tippa dibar yashi.

Hatsarin mota yayi sanadiyar mutuwar mutane 15 a jihar Jigawa
Hatsarin mota yayi sanadiyar mutuwar mutane 15 a jihar Jigawa

Shugaban karamar hukumar Gwiwa, Audu Daurawa, yace duka fasinjojin motar da ta yi hatsari mazauna karamar hukumar Gwiwa ne.

KU KARANTA : Ki ceci rayuwan dan ki – Aisha Yesufu ta shawarci Aisha Buhari

Shugaban hukumar FRSC na jihar Jigawa, Angus Ibezim, ya tabbatar da aukuwan wannan lamari.

Angus Ibezim, yace duka fasinjojin guda 15 wanda ya kunshi mata hudu, maza takwas da kananan yara biyu sun mutu a take a wajen.

Anyi janaizar duka fasinjojin a safiyar ranar Lahadi 31 ga watan Disamba.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng