Har yanzu yan matan Chibok suna cikin zuciyata – Buhari
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci yan garin Chibok su cigaba da hakuri da gwamnati
- Buhari yayi wa yan garin Chibok alkwarin dawo da sauran yan matan chibok da aka sace
Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari, yace har yanzu sauran yan matan Chibok 113 suna cikin zuciyara sa.
Shugaban kasa ya bayyana haka ne a wata sako da ya tura wa yan garin Chibok.
Sanata mai wakiltar mazabar Yammacin Borno, Ali Ndume ya walkici shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya kuma bayyana hanyoyin da gwamnati za ta bi wajen tabbatar da dawo da sauran yan matan Chibok.
KU KARANTA : LABARI DA DUMI-DUMI: Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da dan majalisar jihar Taraba
Shugaban kasa ya bukaci iyayen yan matan da mutanen Chibok su cigaba da hakuri da Gwamnati, saboda ta na iya kokarin ta wajen ganin ta kawo karshen matsalar.
Shugaban kugiyar fafutikar neman dawo da yan matar Chibok, Malam Yakubu Nkeki, ya bayyana farin cikin sa akan sabuwar alkwarin da gwamntin tayi na tabbatar da dawo sauran yan matan Chibok.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng