LABARI DA DUMI-DUMI: Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da dan majalisar jihar Taraba
- An yi garkuwa da dan majalisar dokokin jihar Taraba mai wakiltar mazabar Takum
- A misali karfe 8:45 na daren ranar Asabar aka sace dan majalisar a gidansa da ke Takum
- Wani mai shaida ya ce ‘yan bindiga su shida ne suka kai harin
Wasu ‘yan bindigan da ba a sani ba sun sace Barrister Hosea Ibi, mai wakiltar mazabar Takum a majalisar dokokin jihar Taraba.
Majiyar Legit.ng ta tabbatar da cewar, an sace dan majalisar ne a ranar Asabar, 30 ga watan Disamba a misali karfe 8:45 na dare a gidansa da ke Takum.
Takum ta kasance garin gwamnan jihar, Darius Ishaku.
Wani mai shaida wanda ya yi magana da jaridar Vanguard a kan wayar tarho ya bayyana cewa 'yan bindiga sun kai hari a gidan Barr. Ibi a kan babura.
KU KARANTA: Alkiblar da gwamnati ta zata fuskanta a shekarar 2018 - Inji Gwamnan Adamawa
Mai shaidan ya ce ‘yan bindigar su shida ne suka kai harin.
Har ila yau, ya kara da cewa, 'yan bindigar sun zo ne a lokacin da mamba ya karbi bakwancin wasu ‘yan siyasa da suka kai masa gaisuwar bikin Kirsimeti a gidansa.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng