Gudaddun 'yan Boko Haram sun kaiwa sojoji hari a jihar Yobe
- Wasu mayakan kungiyar Boko Haram sun kaiwa sojoji hari a jihar Yobe
- Sun kai harin ne yayin da suke kokarin tserewa a cikin motocinsu
- Shugaban karamar hukumar Yunusari, Ali Yerima, ya tabbatar da kai harin
Wasu mayakan kungiyar Boko Haram sun kai hari kan sansanin sojojin Najeriya dake garin Kanama, shelkwatar karamar hukumar Yunusari a jihar Yobe.
Shugaban karamar hukumar, Ali Yerima, ya tabbatar da faruwar kai harin. Ya ce mayakan na kungiyar Boko Haram sun shigo garin Kanama da misalin 6:30 na yamma cikin motoci kuma sun wuce kai tsaye sansanin sojojin dake garin inda suka kai harin.
Ya ce ba shi da masaniyar ko an samu asarar rayuka sakamakon kai harin, saidai ya bayar da tabbacin cewar babu wani farar hula da harin ya shafa.
"Bayanin da na samu ya nuna cewar 'yan kungiyar Boko Haram din sun zo cikin motoci Hilux guda bakwai. Sun wuce ta tsakiyar gari ba tare da sun kula kowa ba, saida suka kai inda sansanin sojojin yake sannan suka bude wuta. Saidai sojojin sun mayar da martani ga mayakan," a cewar Yerima.
DUBA WANNAN: Gwamnatin jihar Yobe za ta rabawa ma'aikata bashin N300m domin su kawata gidajensu
Wata majiyar jami'an tsaro ta tabbatar wa da jaridar The Nation cewar mayakan Boko Haram din sun gudo daga jihar Borno ne bayan sun ji wuta daga sojojin Najeriya.
"Idan kun kula, akwai jiragen yaki dake shawagi a sararin samaniyar jihohin Borno da Yobe suna luguden wuta a duk wata maboyar 'yan Boko Haram," kamar yadda majiyar ta sanar.
Kakakin rundunar soji rukunin bataliya ta uku, Kanal Kayode Ogunsaya, bai amsa kira da sakon da jaridar The Nation ta aike masa ba.
Kazalika kwamishinan 'yan sandan jihar, Abdulmalik Sunmonu, ya ce ba zai iya bayar da karin bayani dangane da harin ba saboda "yankin yana karkashin ikon sojin Najeriya ne."
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng