Yi kira a gidan man fetur ka bakwanci gidan yari – Hukumar ‘yan Sanda ta yi gargadi
- Hukumar ‘yan sanda ta ce zata daure duk wanda ta kama da laifin kira na waya ko shan taba a gidajen man
- Hukumar ta ce duk wanda ya aikata wannan laifi za a gurfanar da shi a kan zargin kokarin sa wuta a gidan man
- Jami'in hulda da jama’a na hukumar ya bayyana cewa ba za a bar masu motoci su yi yadda suka ga dama a gidan man ba
Hukumar ‘yan sandan Najeriya ta yi gargadin cewa yin kira da wayar tarho a gidajen man fetur laifi ne kuma duk wanda ya keta dokar zai bakwanci kurkuku.
Babban jami'in hulda da jama’a na hukumar, Jimoh Moshood, ya bayyana hakan, ya ce duk wanda ya aikata wannan laifi za a gurfanar da shi, kuma a ɗaure shi akan zargin kokarin sa wuta a gidan man.
Ya lura cewa 'yan sanda suna da iko su kama duk wanda yake waya ko shan taba a gidajen man fetur.
Kamar yadda Legit.ng ke da labari , Moshood ya bayyana gidajen man fetur a matsayin wurin jama'a inda masu motoci ba za su iya yin aiki kamar yadda suke so ba saboda kayayyakin da ke konewa kamar man fetur da sauran kayayyakin da ake sayarwa.
KU KARANTA: Gwamnatin Tarayya ta yi wa 'yan Najeriya albishir kan lantarki da sufuri
Saboda haka, Moshood ya gargadi jama'a kan saba wa dokokin kare lafiyar al’umma wanda ta hana shan taba da kuma kira na waya a gidanjen man.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng