Dandalin Kannywood: Wakokin fina-finan Hausa 5 da suka fi shahara a shekarar 2017

Dandalin Kannywood: Wakokin fina-finan Hausa 5 da suka fi shahara a shekarar 2017

Hakika wakoki na daga cikin al'adar malam bahaushe inda tun asali aka same shi da su. Sai dai wakokin a wannan zamanin sun canza sabon salo inda mutane suka zamanatar da su ta hanyar yin su da kayan kade-kaden zamani.

Haka zalika ma a bangare guda za ku samu cewa fina-finan Hausa ma da ake yi sukan saka wakokin hausa a cikin su domin nishadantar da masu kallo da kuma sauraro.

Legit.ng ta samu daga BBC Hausa inda ta zakulo wakokin Hausa guda 5 da jama'a su ka fi saurare a wannan shekarar ta 2017, daga cikin dimbin wakoki na mawaka daban-daban.

Wakokin sun shafi jigon soyayya ne da kuma siyasa da biki.

1. UMAR M. SHARIFF (tare da Murja Baba) - "Jirgin So" (daga fim din 'Mansoor')

Wakar "Jirgin So" fito ne a fim din 'Mansoor' na Ali Nuhu. Fitaccen mawaki Umar M. Shariff ne ya rera ta, tare da fitacciyar zabiya Murja Baba.

Haka kuma 'Mansoor' shi ne fim na farko da Umar ya fito a ciki a matsayin dan wasa. Hasali ma dai shi ne jarumin fim din, inda ya fito tare da sabuwar 'yar wasa Maryam Yahya a matsayin jarumar shirin.

An yi ittafaki da cewa babu wata wakar soyayya da ta yi fice kamar ta a bana. An yada ta sosai a kafofin sada zumunta na zamani a yunkurin tallata fim din. Hakan ya sa lokacin da fim din ya fito, matasa sun yi caa zuwa gidajen sinima domin su kalli yadda aka yi rawar wakar.

Dandalin Kannywood: Wakokin fina-finan Hausa 5 da suka fi shahara a shekarar 2017
Dandalin Kannywood: Wakokin fina-finan Hausa 5 da suka fi shahara a shekarar 2017

2. SADIQ ZAZZABI (tare da Maryam Fantimoti) - "Maza Bayan Ka"

Jigon wakar "Maza Bayan Ka" ta Sadiq Zazzabi dai shi ne zambo, ba kambawa ba kamar yadda wasu ke zato.

Duk da yake mawakin bai ambaci wanda ya ke yi wa zambon ba, masu lura da siyasar jihar Kano sun san takaddamar da ake yi tsakanin Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da masu adawa da shi, musamman a jihar inda ya yi gwamna kafin zuwan sa Majalisar Tarayya.

Wakar na kunshe ne da kalamai na muzanta babban abokin adawar Kwankwaso.

Wani al'amari da ya sa wakar ta kara yin fice shi ne kama Sadiq Zazzabi tare da gurfanar da shi a gaban kotu da Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano ta yi a bisa zargin ya saki wakar kafin hukumar ta ba shi takardar izinin fitar da ita.

3. ABDUL D. ONE (tare da Khairat Abdullah) - "Abin Da Ke Cikin Rai Na" (daga fim ]in 'Mansoor')

Wannan wakar ita ce 'yar'uwar wakar "Jirgin So" ta Umar M. Shariff; dukkan su sun fito a fim din 'Mansoor' na Ali Nuhu.

Wakar soyayya ce. Abdul D. One, daya daga cikin yaran Umar M. Shariff, shi ne ya rera ta tare da mawakiya Khairat Abdullah. Wannan waka dai ta fito daga Kaduna, akasin yawancin wakokin zamani da ke fitowa daga Kano.

Abin da ya kara daga wakar shi ne kasancewar ta cikin fim din Ali Nuhu mai suna 'Mansoor' wanda ya na daga cikin manyan finafinan shekarar 2017.

Wannan fim ya sha talla a shafukan sada zumunta, da yake Ali Nuhu, wanda ake yi wa lakabi da Sarkin Kannywood, shi ne ya shirya fim din kuma ya ba da umarni, sannan jarumin shirin, wato Umar M. Shariff, mawaki ne mai dimbin masoya, wadanda ke so su ga yadda ya yi a fim din.

Dandalin Kannywood: Wakokin fina-finan Hausa 5 da suka fi shahara a shekarar 2017
Dandalin Kannywood: Wakokin fina-finan Hausa 5 da suka fi shahara a shekarar 2017

4. DAUDA ADAMU KAHUTU (RARARA) - "Buhari Ya Dawo"

Fitaccen mawakin siyasa Dauda Adamu Kahutu, wanda ake yi wa lakabi da Rarara, ya fitar da wannan wakar ne a daidai lokacin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya dawo daga London, inda ya shafe watanni yana jinya.

Sanin kowa ne an yi ta shaci-fadi kan rashin lafiyar, saboda haka 'yan Nijeriya da dama sun zaku su ga dawowar sa.

Don haka sakin wakar a daidai lokacin na da wuya sai ta karbu a wajen masu saurare.

Rarara ya yi waar ne a matsayin martani ga masu adawa da Buhari, musamman masu cewa rashin lafiyar zai hana shi ci gaba da mulki. Da ma can Rarara magoyin bayan Shugaba Buhari ne.

5. UMAR M. SHARIFF (tare da Khairat Abdullah) - "Rariya" (daga fimdin 'Rariya')

Umar M. Shariff ya ci gaba da rike kambin sa na kasancewa daya daga cikin manyan mawakan wannan zamanin da wakar "Rariya" wadda ta fito a cikin fim din 'Rariya'. Shi da Khairat Abdullah suka rera wakar.

Jigon wakar shi ne soyayya tsakanin saurayi da budurwa. A cewar saurayin, ya yi tankade da rairaya na soyayya da rariya ne, a karshe ya yi dacen samun budurwar tasa a matsayin "tsabar" da wannan tankaden ya samar.

Ya ce: "Tankade na yo na sa rariya, Ke ce ki ka zam tsaba, Zabi na a soyayya." Ita ma ta mayar masa da wadannan kalmomin, tare da nuna masa cewa za ta yi masa sakayya da ba shi zuciyar ta.

Kalmomin soyayya da ake furtawa a wakar sun taba zukatan matasa matuka.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng