Yanzu-Yanzu: Sojojin da yan sanda sun gabza kazamin fada a jihar Ekiti

Yanzu-Yanzu: Sojojin da yan sanda sun gabza kazamin fada a jihar Ekiti

Wasu sojojin Najeriya 'yan asalin jihar Ekiti dake a yankin kudu maso yammacin kasar nan da kuma suka kammala daukar horon su a kwananan sun gabza fada da wasu 'yan sanda dake kan aikin su a jihar ta Ekiti jiya Alhamis.

A yayin fadan nasu kamar dai yadda wani ganau ya shaidawa majiyar mu daya daga cikin sojojin ya yanka dan sanda guda mai suna CPL Abdulkadir yakubu inda ya barshi a nan cikin jini.

Yanzu-Yanzu: Sojojin da yan sanda sun gabza kazamin fada a jihar Ekiti
Yanzu-Yanzu: Sojojin da yan sanda sun gabza kazamin fada a jihar Ekiti

Legit.ng ta samu dai cewa musabbabin fadan shine domin dan sandan yaga sojan yana karbar kudade a hannun jama'ar gari bisa zalunci shine yayi masa magana.

Haka ma dai majiyar mu ta bayyana cewa sojojin da suka kai kimanin mutum 17 suna dawowa ne daga gidan gwamnantin jihar inda suka je ganin gwamnan da ya kirasu.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng