Yanzu Yanzu: Tsohon gwamnan jihar Kebbi, Sa'idu Dakingari da wasu jiga-jigan PDP sun sauya sheka zuwa APC

Yanzu Yanzu: Tsohon gwamnan jihar Kebbi, Sa'idu Dakingari da wasu jiga-jigan PDP sun sauya sheka zuwa APC

Rahotanni dake zuwa mana sun nuna cewa tsohon gwamnan jihar Kebbi, Alhaji Saidu Usman Nasamu Dakingari ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Haka zalika magoya bayan tsohon gwamnan sun mara masa baya wajen sauya shekar. Daga cikin wadanda suka sauya shekar sun hada da tare da tsohon gwamnan akwai Tsohon mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Alhaji Ibrahim K. Aliyu.

Yanzu Yanzu: Tsohon gwamnan jihar Kebbi, Sa'idu Dakingari da wasu jiga-jigan PDP zu sauya sheka zuwa APC
Yanzu Yanzu: Tsohon gwamnan jihar Kebbi, Sa'idu Dakingari da wasu jiga-jigan PDP zu sauya sheka zuwa APC

Sannan akwai tsohon Sakataren Gwamnatin jihar Kebbi Alhaji Garba Rabi'u Musa Kamba, tsohon Shugaban karamar Hukumar Mulkin Birnin Kebbi Alhaji Musa Ibrahim Dan illela, tsohon Shugaban karamar Hukumar Augie Garba Umar Birnin Tudu, tsohon Shugaban Karamar hukumar Mulkin Kalgo Alhaji Abubakar Kuka, tsohon Dan Majalisar Tarayya Hon. Sani Kalgo, tsohon Dan Majalisar Tarayya na Yanzu Zuru Hon. Dan Alkali Durunbun Zuru , tsohowar Yan Yan Majalisar Tarayya ta Yankin Yauri Hon. Halima Hassan Tukur.

Har ila yau cikin masu sauya shekar akwai Alhaji Abubakar Sadik Yalwa Katikan Yauri, Ummaru Maye Yauri , Lawali Na Malam Dakin Gari, Alhaji Shehu Ma'azu Zuru, Alhaji Zayyanu Maigishiri.

KU KARANTA KUMA: Abinda muka tattauna da Buhari – Abdulmumini Jibrin

Duk sun ce sun bar Jam'iyar PDP sun koma jam'iyar APC bayan la'akari da kwazon jam'iyyar APC karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma kwazon Gwamnan jihar Kebbi, Sanata Atiku Bagudu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng