Wulakanta Al-Kur’ani baya biya wa al’umma bukatunsu na duniya
- Shugaban hukumar Hizba na jihar Zamfara yayi gargadi akan wulkanta al-kura'ani
- Allah yana daukaka mutum a duk inda yana daraja al-kur'ani inji Atiku Balarabe
- Dakta Atiku Balarabe Zawiyya ya ce Al-kurani rahama ce ga al'umma
Shugaban hukumar Hizba na jihar Zamfara, Dakta Atiku Balarabe Zawiyya, yace, wulakanta Al-ku’rani baya biya wa al’umma bukatar su ta duniya,
Atiku yace masu jefa al’kur’ani cikin masai da share bayan gida da shi dan samun duniya, wallahi bata samuwa.
Kuma duk wanda hukuma ta kama shi yana aikata wannan mumunar abu zai gamu da hukunci mai tsanani inji Atiku.
Dakta Atiku ya bayyana hake ne a wajen taron zagayan bikin Maulidi da yagabata a birinin Gusau.
KU KARANTA : Dokar haramta kida a Zamfara na fuskantar turjiya
“Al-Kur’ani ba abun wasa bane, wannan littafi rahama ce ga al’ummar musulmi, kuma masu neman abun duniya da mukaman siyasa kada idanunsu su makance su fada cikin fushin Allah.
"Muna kira ga masu wulakanta Al-Kur’ani da su ji tsoron Allah su sani cewa karantawa shi ake yi, Allah yana daukaka mutumin da ya daraja al-kur'ani a duk inda yake.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng