Najeriya za ta sayi jiragen yaki na zamani a kan $593m daga kasar Amurka
- Hukumar sojin saman Najeriya ce ta sanar da hakan
- A watan Fabrairu ake saka ran za'a kammala duk matakan siyen jiragen
- Jakadan Amurka a Najeriya ya ce tabbatar da tsaro a Najeriya abu ne mai muhammaci ga Afrika
Hukumar sojin saman Najeriya ta sanar da cewar gwamnatin Amurka ta amince da siyarwa Najeriya wasu jiragen yaki na zamani domin cigaba da yaki da aiyukan ta'addanci.
Jiragen da za'a siya kirar 12 A29 Super Tucano, na dauke da makamai da wasu ragowar kayan aiki na musamman.
Hukumar sojin sama ta bayyana cewar Amurka za ta siyarwa da Najeriya jiragen a kan kudi miliyan $593.
DUBA WANNAN: An tafkawa shahararrun mawakan Najeriya biyu sata a cikin jirgin sama
Jakadan kasar Amurka a Najeriya ne ya mika wasikar amincewar Amurka na sayar wa da Najeriya jiragen ga hukumar sojin sama a jiya Laraba. Kazalika Jakadan ya ce tabbatar da tsaro a Najeriya yana da matukar muhimmanci ga kafatanin kasashen Afrika ta yamma.
Darektan hulda da jama'a na hukumar sojin sama ta kasa, AVM Olatokunbo Adesanya, ya ce za'a kammala biyan kudin jiragen yakin kafin ranar 20 ga watan Fabrairu, shekarar 2018.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng