Hotunan yadda soji biyu suka yiwa wani mutum zigidir a jihar Legas
Shafin Premium Times ya ruwaito cewa, na'ura ta daukar hoto ta cafko wasu soji biyu a yayin da suke lakadawa wani mutum duka tare da tube masa kaya.
Wannan lamari ya afku ne a kasuwar Ajah dake jihar Legas a ranar Talatar da ta gabata, inda sojin biyu suke yi barazanar yanke mazakutan mutumin yayin da suke tafkarsa a bayyanar jama'a.
'Yan kasuwar da dama sun gaza bayar da rahoto kan wannan al'amari na keta haddi a sakamakon fargaba ta ko sojin na iya kai musu nasu harin.
KARANTA KUMA: Ni ba cikakkiyar budurwa ba ce amma ban taba aure ba – Rahama Sadau
Sai dai wani mai sayar da shinkafa da bai bukaci a bayyana sunan sa ba, yace wannan mutumi matukin babur mai kafa uku ne, kuma ya bangaje daya daga cikin sojin a yayin da yake tuki.
LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng