Cikakken bafullatanin Gembu ya yi zarra a hukumar rundunar sojin Najeriya
- Birgediya Janar Abubakar Adamau ya ciri tuta
- Wani cikakken bafullatanin ne asali daga garin Gembu
- Gwarzon mayakin dai ya fito ne daga kabilar Wuro-Ardo Yuguda /Leme Da'u
Wani cikakken bafullatanin asali daga garin Gembu a karamar hukumar Sardauna ta jihar Taraba Mai suna Abubakar Adamau ya ciri tuta inda ya taka matsayin Birgediya Janar a hukumar rundunar sojin kasa na Najeriya.
Gwarzon mayakin dai ya fito ne daga kabilar Wuro-Ardo Yuguda /Leme Da'u a a can wata ruga dake a garin na Gembu kuma matsayin da ya taka shine na biyu rak daga karamar hukumar ta sa ta Sardauna.
Legit.ng ta samu kuma cewa shine mutum na farko daga karamar hukumar ta Sardauna da ya halarci makarantar koyon dabarun yaki ta Jihar Pennsylvania a can kasar Amurka.
dan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng