Yanzu bama iya wasa da dariya da shugaba Buhari - El-Rufa'i
- Gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufa'i ya ce yanzu basa samun damar wasa da dariya da shugaba Buhari
- Ya ce a baya su kanyi birgima a kasa a falon Buhari duk cikin raha
- Shugaba Buhari na shan yabo a wurin hadimansa na kusa da shi
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i, ya bayyana cewar yanzu basa iya samun damar wasa da dariya da shugaba Buhari kamar yadda suka yi a baya, lokacin da suke jam'iyyar adawa.
El-Rufa'i ya ce shi da wasu da dama, da be ambaci sunan su ba a cikin gwamnatin, sun rasa wannan dama yanzu.
Gwamnan ya bayyana shugaba Buhari a matsayin mutum mai barkwanci. Wannan magana da Elrufa'i ke yi na daga cikin wani bangare na faifan bidiyo da akan wasu halayen Buhari da jama'a basu sani ba kuma ake saka ran za'a nuna a gidajen talabijin na NTA da Channels a ranakun Litinin da Talata.
DUBA WANNAN: Osinbajo, Elrufa'i, da Fashola sun bayyana halayen shugaba Buhari da jama'a basu sani ba
Makusantan shugaba Buhari sun yi ruwan kalaman yabo a kan kyawawan shugaban kasar.
Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, Ministan Aiyuka Lantarki da Gidaje, Babatunde Raji Fashola, Gwamnan jihar Ogun, Ibikunle Amosun, da mai bawa shugaban kasa shawara a kan harkokin kasashen ketare, Abike Dabiri-Erewa, duk sun tofa albarkacin bakinsu a cikin tsakuren faifan bidiyon.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://facebook.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng