Dandalin Kannywood: Samun mazan da za su aure mu yanzu yayi wuya - Rashida Adamu

Dandalin Kannywood: Samun mazan da za su aure mu yanzu yayi wuya - Rashida Adamu

Fitacciyar tsohuwar jarumar nan ta fina-finan Hausa a masana'antar Kannywood kuma 'yar siyasa mai suna Rashida Adamu ta bayyana cewa suna matukar shan wahala yanzu wajen samun mazajen aure.

Jarumar dai ta bayyana hakan ne a 'yan kwanakin nan kamar dai yadda muka samu daga majiyar mu inda kuma aka ruwaito cewa ta bayyana cewa a duk lokacin da ta samu mijin aure, to fa da gudu zata aure shi.

Dandalin Kannywood: Samun mazan da za su aure mu yanzu yayi wuya - Rashida Adamu
Dandalin Kannywood: Samun mazan da za su aure mu yanzu yayi wuya - Rashida Adamu

Legit.ng dai ta samu cewa majiyar tamu ta ruwaito jarumar na cewa: "Samun Mazan Ne Da Wahala, Amma Ko Yanzu Na Samu Miji Da Gudu Zan Yi Aure".

Mai karatu dai zai iya tuna cewa jarumar tuni ta dauke kafar ta daga fitowa a matsayin jaruma a cikin fina-finai sannan kuma ta tsunduma cikin harkokin siyasa inda daga baya ma har ta samu mukamin mai bayar da shawara ga Gwamnan jihar ta Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng