Anka: Masarautar Anka ta tara makuddan kudi don tallafawa harkokin ilimi da marayu
- Masarautar Anka a jihar Zamfara ta tara makuddan kudi don tallafawa harkokin ilimi da marayu
- Rahotanni sun bayyana cewa an tara wannan makuddan kudin ne don ci gaban masarautar Anka
- Gwamna Abdul'aziz Yari ya yaba wa masarautar don shirya tsarin da zai taimakawa kokarin gwamnati a jihar
Gidauniyar Masarautar Anka wato ‘Anka Emirate Foundation’ a jihar Zamfara a ranar Asabar, 23 ga watan Disamba ta tara kudi N91 miliyan don tallafawa harkokin ilimi da marayu da marasa galihu da matasa da kuma mata a fadin jihar.
Jaridar NAN ta ruwaito cewa an tara wannan makuddan kudin ne don ci gaban masarautar Anka a yankin karamar hukumar Anka.
Majiyar Legit.ng ta tabbatar cewa manyan ‘yan siyasa da 'yan kasuwa da kuma mutane masu hannu da shuni daga masarautar sun ba da gudummawa daban-daban ga shirin.
Rahotanni sun nuna cewa tsohon gwamnan jihar kuma sanata mai wakiltar jihar Zamfara ta yamma, Alhaji Ahmad Sani-Yarima, wanda shine babban banki a taron, ya ba da N10 miliyan.
KU KARANTA: Taron sirri da Sanatocin arewa suka shiga, me suka kulla?
Sauran manyan masu bayarwa sun hada da gwamnatin jihar da Kwamishinan kananan hukumomi da harkokin sarakunan gargajiya, Alhaji Muttaka Rini, wadanda suka ba da tallafin N10 miliyan kowane.
Gwamnan jihar Zamfar, Abdul'aziz Yari ya yaba wa masarautar don shirya tsarin da zai taimakawa kokarin gwamnati na kokarin inganta rayuwa da harkokin ilimi ga wadanda zasu ci gajiyar shirin.
Yari, wanda Rini ya wakilta, ya yaba da kokarin masarautar wajen tallafawa ci gaba da bunkasa matasa, yara da mata.
Sarkin Anka, Alhaji Attahiru Ahmad, ya gode wa mutanen masarautar akan tallafawa da kuma hadin kai ga Gidauniyar da sauran ayyukan masarautar.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng