Yakin Duniya na barazana ga duniya, inji wani babban sojin Amurka

Yakin Duniya na barazana ga duniya, inji wani babban sojin Amurka

Wani babban Janar na Sojin Amurka ya ce yana tsoron nan ba da dadewa ba, duniya zata tsunduma cikin rikici da zai kaita ga yaki, musamman a yankin tekun pacific, teku da ke tsakanin AMurka, Rasha, Chana da Japan.

Yakin Duniya na barazana ga duniya, inji wani babban sojin Amurka
Yakin Duniya na barazana ga duniya, inji wani babban sojin Amurka

Robert Neller dai shine babban kwamandan sojin Amurka, kuma yana wakiltar Amurka ne a taron sojin ruwa na kasar Norway mai sanyin yanayi.

Neller, yace a yankin Pacific, inda manyan kasashe masu karfin soji ke zari-zuga, yafi tsoron rikicin na iya kaure wa.

A cewarsa; "Ku yi taka tsantsan.Kowa ya daura damararsa.Domin akwai babban yakin da ke shirin barkewar a tekun Pacific.Ku maida hankalinku ga kasar Rasha.Saboda kwai sojoji 300 na Rasha wadanda ke kallon ku dare da rana.

Yawansu zai iya kai dubu 3 a dare 1 ba tare mu farga da hakan ba.Ku ma kar ku rumtsa, ku dinka sa ido game dukannin ababen da suke yi. Idan ban bata a lissafina, mumman yaki na gab da rutsawa da duniya"

DUBA WANNAN: Dansanda ya karbi mari zazzafa a hannun soja

A shekarun nan dai, dangantaka tsakanin manyan kasashen duniya na kara tsami, kuma ana samun barazanar soji da makamai daga kasashe zuwa ga wasu.

Kasar Koriya ta shamal ma dai, ta sha barazanar yaki kan Amurka, kuma tana ta gwajin makamai na nukiliya da rokar da ka iya kaiwa kowanne birni a Amurka.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng