An tashi ci 3-0 tsakanin Madari da Barsa a wasan La-Liga na dazunnan

An tashi ci 3-0 tsakanin Madari da Barsa a wasan La-Liga na dazunnan

Kwallo Kafa: An tashi ci 3-0 tsakanin Madrid da Barca a wasan LaLiga na dazunnan. Wasan na cikin gida dai a kasar ta Spain, yafi kowanne daukar hankali a duniya

An tashi ci 3-0 tsakanin Madari da Barsa a wasan La-Liga na dazunnan
An tashi ci 3-0 tsakanin Madari da Barsa a wasan La-Liga na dazunnan

An kayar da Madrid gidan kwallo a cikin gida a wasansu na dazu da kishiyoyinsu na Barcelona. Dama dai a duniya kulob din guda biyu ke fini-in-fika, a 'yan shekarun nan.

Suarez ne ya zura kwallon farko a zagaye na biyu na wasan, sai Messi ya zura ta biyu a bugun fenareti, saboda kade kwallon da dan wasan Madrid yayi da hannu, bayan ta kusa shiga raga.

Lafari dai ya bashi jan kati, kuma ya baiwa Barsalona bugun daga kai sai gola, mai tsaron gida.

DUBA WANNAN: David Mark ya shiga uku

Aleix Vidal ya zura ta ukku dab da za'a tashi, a wasan mai kayatarwa, wanda ya rikita masoya kwallo a duniya.

Real Madrid dai bata ci ko kwallo daya ba, ita kuwa Barcelona ta ci ta har ukku a wasan na derby, wado na kishiyoyin cikin gida.

Samari har da 'yan mata dai a Najeriya suna mayatar son kwallon kafa, musamman saboda sai ka sani sannan ka zamo cikin wayayyu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng