An fitar da Sarauniyar kyau a Najeriya na shekarar bana
- An yi gasar sarauniyar kyau a bana
- Wata 'yar Adamawa ce ta lashe gasar
- Wasu na ganin rashin tarbiyyar lamarin
Budurwa Mildred Ehiguese, son kowa kin wanda ya rasa, a bana dai ita ta dauki lamba daya ta wadda tai kowa kyau a Najeriya.
Budurwar ta fito ne daga jihar Adamawa. An kammala gasar ne a jiya a jihar Legas. Kuma ita ta gaji Chioma Obiadi ta Anambra, a bara, wadda aka yi ta cece kuce kan bidiyo na masha'a da tayi da kawaye ana madigo.
DUBA WANNAN: Za'a zamanantar da tashishin sadarwar Kaduna
Daily Times ce dai ta dauki nauyin bikin, wanda aka yi a Eko Hotels, otal da yafi kowanne armashi a Najeriya.
Koda yake a baya jihohin Kano da Zamfara sun kaurace wa gasar, daga baya sun koma suna shiga gasar, kuma a bana ma sun halarta, kuma sun tura wadda zata wakilci jama'arta.
Shekaru 60 kenan dai da aka fara irin wannan gasa domin karfafa mata, kamar yadda masu daukar nauyin shirin suka ce.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng