Dandalin Kannywood: Bana bukatar a ci gyara na a turanci - Adam A Zango
Shahararren jarumin finafinan wasan hausa, Adam Abdullahi Zango, ya bayyana fushinsa akan mutane da suke cin gyaran sa a yaren turanci a duk lokacin da ya furta a baka ko kuma ya rubuta a dandalan sada zumunta.
Fitaccen jarumin na Kannywood, wanda ya shahara da sunan Fresh Prince ya bayyana a ranar Jumma'ar da ta gabata cikin wani bidiyo a shafinsa na sadar zumuntar instagram, inda ya nemi mutane akan su daina cin gyaransa a turanci.
Cikin fushi a yaren turanci, jarumin yace baya bukatar gyaran kowa na kowane irin nau'i a fannin rubutu ko furta yaren turanci
Yake cewa, "zan yi wasu kalami tare da masaniyar zasu fusatar da masoya na, makusanta da abokan arziki, akan su daina cin gyara na a turanci domin babu wanda na baiwa labarin nayi makaranta, akan tituna na tsinci wanda na iya a halin yanzu."
Legit.ng ta ruwaito da sanadin jaridar Daily Post cewa, jarumin ya hallara a wasu finafinai na Kannywood da suka hadar da; Gwaska Returns, Hindu da Bayan Rai, inda yace ya furya yaren turanci ne a cikin wadannan shiri domin ya isar da sakonsa ga wadanda basu jin yaren hausa.
KARANTA KUMA: Rarrabuwar kawunan lauyoyi ta faskara sanadiyar kamun da EFCC ta yiwa shugaban kamfanin Innoson
Jarumin ya ci gaba da cewa, bai ga dalilin yiwa turancin sa kima ko awo ba domin kuwa cikin yaren hausa suke shirya finafinansu.
Ya kara da cewa, "tabbas na samu nasarori a wannan fagge, saboda haka masu cin gyara su kama gabansu domin yin abinda ya shafe su, kuma su barni na sarara. Bana bukatar gyaransu. Kuje can ku ci gyaran wadanda suka yi nazarci yaren turanci domin ni kuwa ban iya furta shi a baka ba ballanta a rubuce."
LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng