Nauyin bashi ya sanya an tursasa 'yar shekara goma auren wani dattijo dan shekara 50 a duniya

Nauyin bashi ya sanya an tursasa 'yar shekara goma auren wani dattijo dan shekara 50 a duniya

Rahotanni daga shafin jaridar Daily Mail sun bayyana cewa, jami'an tsaro na 'yan sanda sun ceto wata yarinya 'yar shekara 10 da mahaifiyarta ta aurar da ita ga wani dattijo dan shekara 50 domin samun damar biyan bashi na kudi da suka tasar ma £3,400.

Jami'an 'yan sandan sun dirra a farfajiyar daurin auren a yayin da wannan dattijo, Jeetmal Mehar, ya bayar da sadakin £5,400 domin auren diyar cikin sa, Pathani Mangrio, inda suka yi cafke kimanin mutane 11, sai dai anyi rashin sa'a angon, Muhammad Mehar ya arce.

Gulzar Mari, jami'in dan sanda mai fadi tashi akan wannan lamari ya bayyana cewa, da misalin karfe 11:00 na safiyar ranar 19, ga watan Dasumba ne suka samu rahoton cewa za a aurar da karamar yarinya ga tsoho dan shekara 50 a duniya.

Wannan rahoton ne ya sanya basu yi wata-wata ba suka dugunzuma har farfajiyar wannan bikin buduri, inda suka cafko mutane da dama da suka hadar da mahaifiyar wannan yarinya da ita kan ta amaryar.

Masmat Nabiat tare da amarya Pathani
Masmat Nabiat tare da amarya Pathani

Masmat Nabiat, wadda ita ce mahaifiyar amaryar ta bayyana cewa, ta amince da aurar da diyar ta ga tsohon domin samun damar biyan bashi na kimanin £3,400 da yayi musu katutu.

KARANTA KUMA: Majalisar dattawa ta kammala duk wata gudawarta a shekarar 2017

Jami'an 'yan sanda sun tambayi Masmat inda mahaifin yariyar yake, sai ta labarta musu cewa ai sakamakon ciwon kafafu da yake fama da shi bai iya halartar daurin auren ba.

A yayin tuntubar mai daura auren, Qazi Haji Solangi, ya bayyana cewa bashi da masaniyar shekarun amaryar ko angon ta domin kuwa sunayen su da na mahaifansu kawai ya bukata.

Legit.ng ta fahimci cewa, jami'an 'yan sandan sun mika wannan lamari gaban kotu ta birnin Sindh a ranar Larabar da ta gabata domin zartar da shari'a kamar yadda dokokin kasar suka tanadar.

LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng