Dandalin Kannywood: Har yanzu ban san dalilin da yasa aure na ya mutu ba - Jaruma Maryam Isah
Fitacciyar jarumar nan a masana'antar shirya fina-finan Hausa da ake yiwa lakani da Kannywood sannan kuma kanwa da tsohuwar jarumar nan ce kuma matar jarumi Sani Danja watau Mansura Isa mai suna Maryam Isah ta bayyana cewa har yanzu bata san ainihin dalilin mutuwar auren ta.
Jarumar dai ta yi wannan ikirarin ne a yayin da yake yin fira da majiyar mu lokacin da take ansa tambayoyi game da mutuwar auren nata.
Legit.ng har ila yau ta kara da cewa mutane da dama sukan nuna suna son 'yan fim ba don Allah ba sai dai kawai don suna tunanin suna da kudi ko kuma kyau a maimakon soyayya to sai su biyo ta hanyar aure.
Jarumar ta kara da cewa da zaran sun samu nasarar auren na su suka kuma samu abunda suke nema sai kawai su rika takalar rigima duk don su rabu da su.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng