Bayan shafe shekaru babu haihuwa: Wata mata a jihar Naija ta haifi 'yan hudu ta hanyar dashen kwayayen halitta

Bayan shafe shekaru babu haihuwa: Wata mata a jihar Naija ta haifi 'yan hudu ta hanyar dashen kwayayen halitta

- Ta haifi 'yan hudu bayan ta shafe shekaru 17 da aure babu haihuwa

- Ta samu haihuwar be ta hanyar yi mata dashen kwayoyin halitta

- Daya daga cikin jariran ya mutu

Wata ma'aikaciyar asibiti, Hadiza Ndayebo, ta haihu 'ya'ya hudu rigis a asibitin Babangida Aliyu dake garin Minna bayan ta shafe shekaru 17 da aure babu haihuwa.

Hadiza ta bayyanawa manema labarai cewar ta samu ciki ne ta hanyar yi mata dashen kwayayen halitta bayan data shafe shekaru 17 da aure babu haihuwa.

Bayan shafe shekaru babu haihuwa: Wata mata a jihar Naija ta haifi 'yan hudu ta hanyar dashen kwayayen halitta
Wata mata a jihar Naija ta haifi 'yan hudu ta hanyar dashen kwayayen halitta

"Na zabi yin dashen kwayayen halittar ne saboda rashin samun ciki ta hanyar da aka fi sabawa da ita. Na taba samun ciki a baya amma kafin na kai ga haihuwa sai nayi bari. Tun bayan wancan lokacin, shekaru goma, ban kara samun wani cikin ba." Inji Hadiza.

DUBA WANNAN: An yankewa wasu dalibai 'yan Najeriya hukuncin kisa a kasar Malaysia

Hadiza ta kara da cewar; babu wanda ya dauketa da muhimmanci lokacin data fadawa abokan zamanta cewar anyi mata dashen kwayayen halittar amma sai gashi yanzu cikin ikon ALLAH ta haife 'ya'yanta lafiya. Hakazalika ta bayyana yadda ta sha takaici da kalubale a kan rashin samun haihuwa shekaru 17 bayan aure.

Mijin Hadiza, Alfa Mamood, ya bayyana farincikinsa bisa wannan kyauta da ALLAH ya yi masu tare da bayyana cewar sakayya ce ubangiji ya yiwa matar tasa bisa hakuri da juriya data nuna.

Wata daga cikin ma'aikatan asibitin da suka karbi haihuwar Hadiza, Comfort Tsado, ta ce wannan shine karo na farko da aka haifi 'yan hudu asibitin duk da dai daya daga cikin jariran ya mutu daga baya.

Hadiza ta shafe tsawon watanni bakwai tana kwance asibiti, kafin ta haihu, domin kulawa ga juna biyun da take dauke da shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng