Hukumar fasa kwabri (Nigerian Customs) ta yi bayyani akan daukan ma'aikata
- Hukumar fasa kwabri ta ce bata fara daukan masu aiki ba
- Joshua Angbalaga ya ce idan lokacin daukan ma’aikata yayi hukumar za ta sanar da yan Najeriya
- Angbalaga ya garagadi masu neman aiki ruwa a jallo akan fadawa hanun yan cuwa cuwa saboda neman aiki
Kwantrolla hukumar fasakwabri (NCS) reshen jihar Borno da Yobe, Joshua Angbalaga yayi bayyani akan daukan masu aiki da hukumar za ta yi.
Joshua Angbalaga ya fadawa manema labaru a Maiduguri baban birnin jihar Borno cewa rahoton daukan maa’ikata karyace.
Yace idan lokacin daukan aiki yayi, hukumar za ta sanar da yan Najeriya ta hanyoyin da ya dace.
KU KARANTA : Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 3 sun kashe mutun 1 a jihar Niger
Kwantrolla ya garagadi masu neman aiki ruwa a jallo da su bi a hankali dan kada su fada hanun yan cuwa cuwa da sunan neman aiki.
“Duk wani mutumin da yace yana da karfin ba matasa aiki a hukumar NCS makaryaci ne,” inji Joshua Angbalaga.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng