Rashin adalci da talauci suke ta'azzara ta'addanci a Najeriya - Shugaban ASUU

Rashin adalci da talauci suke ta'azzara ta'addanci a Najeriya - Shugaban ASUU

Kungiyar ma'aikatan jami'o'in Najeriya (ASUU), ta bayyana cewa rashin adalci da 'yan Najeriya ke fuskanta daga shugabanni 'yan siyasa shike jefa da yawansu ciki ta'addanci na yaki da kasa.

Shugaban kungiyar, Farfesa Biodun Ogunyemi, shine ya bayyana hakan a ranar Larabar da ta gabata a babban birni na Ibadan dake jihar Oyo, inda yace Najeeriya zata ci gaba da fuskantar kalubale na ta'addanci muddin gwamnatin shugaba Buhari bata tashi tsaye ba akan matsaloli na rashin adalci dake kawo kasar nan koma baya.

Farfesa Biodun Ogunyemi
Farfesa Biodun Ogunyemi

Yake cewa, rashin adalcin da 'yan Najeriya ke fuskanta daga shugabanni sun hadar da; rashin kulawa da bukatunsu kama daga harkokin ilimi, lafiya, rashin wadatattun hanyoyin na gine-gine dake saukaka matsi na rayuwa da kuma rashin aikin yi a fadin kasar.

KARANTA KUMA: Karkatar da tankoki 144 na dakon man fetur a jihar Kano: Kungiyar IPMAN ta karyata rahoton

Ogunyemi ya jadda cewa, babu kasar ta zata samu zaman lafiya da kwanciyar hankali matukar mafi yawan al'ummarta suna fuskantar barazana ta talauci a yayin da 'yan siyasa da shugabanni ke yin sama da fadi da kudaden al'umma domin kawunansu da iyalansu kadai.

Farfesan ya kara da cewa, abin takaici ne da kuma baƙin ciki a ce gwamnatin shugaba Buhari tana ci gaba da dan yafitawa bangaren ilimi wasu kudade da basu taka kara ba balle su karya shi.

LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng