Ashsha! Wani Dangaruwa bahaushe ya kekketa maƙogoron budurwarsa a Legas
Wani matashin dan garuwa, Ibrahim Useni da yayi ma budurwasa yankan rago ya gurfana a gaban kuliya manta sabo, kotun majistri dake Ebute Meta na jihar Legas.
Dansanda mai kara, Chinalu Uwadione ya bayyana ma kotu cewa Ibrahim mai ruwa ya kashe budurwar tasa mai suna Jenifer Odiase ta hanyar yi mata yankan rago a Otal din Harry dake Badagry, ranar 25 ga watan Nuwamba da misalin karfe 2 na rana.
KU KARANTA: Rikita rikitan sanya ɗan-kwali a Kotun ƙoli Najeriya: Yarinyar Abiola ta jinjina ma Lauya Firdausi
Inspekta Chinalu ya shaida ma Kotu cewa Ibrahim Mai ruwa ya yi amfani da wuka ne wajen yanka wuyan Jennifer, sakamakon budurwar ta cinye masa kudaden dayake bata ajiya, kamar yadda kamfanin dillancin labaru ta ruwaito, NAN.
“Ibrahim ya nemi budurwa tasa ta bashi kudaden dayake bata ajiya a duk rana idan ya dawo daga aikin siyar da ruwa, amma sai budurwar ta ce masa babu ko sisi, nan take Ibrahim ya ciro wuka ya yanka mata wuya.” Inji Inspekta Chinalu
Bayan sauraron dukkan bangarorin, sai Alkali A.S Okubule ya umarci a garkame mai laifin, zuwa lokacin da zai samu karin haske daga ofishin babban mai shigar da kara na jihar Legas, DPP.
Daga karshe ya Alkali Okubule ya dage sauraron karar zuwa ranar 19 ga watan Janairun 2018.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng