Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 3 sun kashe mutun 1 a jihar Niger
A safiyar ranar Talata, 19 ga watan Disamba, wasu yan bindiga sun kai hari kauyen Gidan Banobi a yankin Zazzaga, a karamar hukumar Munya dake jihar Niger, sunyi garkuwa da mutane uku sannan suka kashe mutum daya, a cewar yan kauyen.
Majiyarmu ta bayyana cewa an harbe Musa Adamu mai shekaru 54 da haihuwa har lahira don fuskantar masu garkuwan da yayi bayan sun cafke matarsa da yayansa guda biyu a lokacin da suka kai hari kauyen da misalin karfe 2 na dare.
Wannan harin ya kasance hari na uku da aka kai a yankin a cikin sa’o’i 72.
Hakimin Zazzagawa, Musa Umoru ya fada wa manema labarai ta wayar talho cewa kauyen ta tara kudi naira miliyan 10 a matsayin kudin fansa ga 5 daga yan kauyen guda 10 da aka yi garkuwa da su kafin aukuwan wannan al’amarin kuma a Gidan Banobi.
Yace masu garkuwan sun saki Amina Mohammed mai shekaru 60 da haihuwa a hanya, sannan suka bata lambar wayansu don kaiwa iyalen wadanda suka yi garkuwa dasu don yarjejeniya.
“A halin da ake ciki mutane na cigaba da kwashe kayansu don hijira zuwa kauyuka da muke makwabtaka dasu saboda har yanzu gwamnati ta ki kawo mana taimako da tallafi.
“Mutane na sun gama siyar da kayansu don biyan kudin fansa, har da kayan gona, mun kai korafe-korafe ga yan sanda amman basu dauki mataki game da al’amarin ba”.
Hakimin ya bayyana damuwar cewa kauyen Zazzaga mai yawan yankuna 50 tare da yawan mutane 2000 ta kasance da ofishin yan sanda guda daya tare da yan sanda guda biyu, ya kuma bukaci hukumomi da su duba wannan al’amarin.
KU KARANTA KUMA: Hukumar 'yan sanda ta cafke 'yan fashi da makami hudu a jihar Jigawa
Mai magana da yawun hukumar yan sanda ASP Peter Sunday ya tabbatar da aukuwar al’amarin amman yace an tura rundunar yan sanda da na sojojin Najeriya don maido da zaman lafiya ga yankin.
LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng