Abin nema ya samu: Dan fansho ya lashe kyautar miliyan daya a gasar banki

Abin nema ya samu: Dan fansho ya lashe kyautar miliyan daya a gasar banki

- Dan fansho ya yi nasarar lashe kyautar miliyan daya a gasar banki

- Dan fansho, Bello Sarafa, tsohon ma'aikacin kamfanin wutar lantarki ne

- Bankin Skye ne ya gudanar da gasar

Wani tsohon ma'aikacin kamfanin wutar lantarki (PHCN), Bello Sarafa, ya yi nasarar lashe kyautar miliyan daya a gasar karkaden bankin Skye ta 'Reach for the Skye millionaire Reward' da aka gudanar a karshen satin da ya gabata.

Abin nema ya samu: Dan fansho ya lashe kyautar miliyan daya a gasar banki
Abin nema ya samu: Dan fansho ya lashe kyautar miliyan daya a gasar banki

Manyan mutane da masu ruwa da tsaki a harkokin kudi da suka halarci taron karkaden da bayar da kyauta ga wadanda suka yi nasara sun yabawa bankin bisa kokarin sa na kara karfin gwuiwa ga masu karafin karfi.

DUBA WANNAN: Yunwa zata kashe iyalan mu: 'Yan sandan da suka shafe watanni babu albashi sun koka

Abokanan huldar bankin da dama ne suka tururuwar zuwa Iyana Ipaja domin shiga gasar bankin da a karshe Mista Sarafa, Dan fansho da ya shude fiye da shekaru 12 yana ajiya a bankin, ya yi nasarar lashe gasar.

Babban manajan bankin, Mista Tokunbo Abiru, da shugaban tsare-tsare na bankin, Nnduneche Ezurike, ya wakilta bayar da tabbacin cewar Bankin zai cigaba da kyautatawa abokan huldar sa domin basu karfin gwuiwar cigaba da ajiya a bankin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a:

labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng