Rikita-Rikita: Kasashen Rasha da Sin na shirin kai wa Amurka wani harin hadin gwiwa
Wasu fitattun tsaffin sojojin kasar Amurka sun bayyana cewa akwai yiwuwar kasashen Sin da Rasha su kai wa kasar Amurka wani harin hadin gwuiwa idan har fada ya barke a makwafciyar su ta kasar Koriya da yanzu haka ke fadan cacar baki da ita Amurka din.
Haka ma dai wani babban soja na kasar ta Koriya ta Arewa mai sunan Laftanal Janar Hongguang da ke zaman tsohon kwamanda a yankin Nanjing na yamma ya yi hasashen cewa yaki tsakanin kasar da Amurka na iya barkewa daga yanzu zuwa watan Maris na shekara mai kamawa .
Legit.ng dai ta samu cewa jami'in sojin Hongguang ya bayyana hakan ne a yayin da yake zantawa da shugabannin jaridar nan ta yankin shugabannin mulkin gurguzu na 'The Global Times'.
Haka ma dai jaridar ta yan gurguzun ta kuma ruwaito wani babban jami'in sojan kasar Sin kuma fitaccen mai sharhi kan al'amurran yau da kullum mai suna Song Zhongping ya na cewa ita ma kasar ta Sin da kuma Rasha ka iya tsoma kan su cikin fadan idan har yiwuwar hakan ta faru.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng