Sojoji a bariki sun koka wai Samari basa neman yayansu Mata
- Sojojin Najeriya mazauna barikin Sojin bukavu sun koka kan maza basa neman auren yayansu
- Sojojin sun roki samari da su fara zuwa zance don neman auren yayansu
Sojojin Najeriya dake zaune a barikin Bukavu dake jihar Kano sun koka tare da nuna bacin rai game da yadda samari basa shiga bariki neman matansu da nufin aure.
Wanna korafi ya fito ne daga bakin babban limamin Masallacin juma’a dake cikin barikin, inda yace akwai yan mata da dama a cikin barikin da suka isa aure, amma maza na tsoron zuwa neman su aure.
KU KARANTA: Na kaɗu matuƙa da zarge zargen da mataimakin gwamna ya yi – Inji Gwamna Ganduje
Rariya ta ruwaito Limamin yayi wannan batu ne a yayin bikin yaye wasu dalibai guda 40 da suka yi sauka a islamiyan dake cikin barikin, sa’anna ya kara da kira ga jama’a da su dinga shigowa barikin don neman aure yayansu mata.
Legit.ng ta samu rahotanni dake nuna samari na tsoron shiga bariki ne da niyyar neman aure don gudun wulakanci da kuma cin zarafi daga wajen jami’an Sojoji musamman kuratan dake gadin bariki.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng