Wata ɓarauniya data shahara wajen satan kananan yara a Masallaci ta shiga hannu
Jami’an rundunar Yansannda jihar Legas sun kama wata mata dake satar kananan yara a Masallaci, Juliet Ajagun, mai shekaru 38, inda suka gurfanar da ita gaban kuliya manta sabo.
Premium Times ta ruwaito jami’in dansanda mai shigar da kara, Clifford Ogu ya bayyana ma Kotu cewar Juliet ta saci wannan yaron ne a wani Masallaci dake titin Muyi Opalaye, Unguwar Ikeja a lokacin da Uwar yaron ke Sallah.
KU KARANTA: An kama wani matashi yayinda yake yunkurin yin kudin jini da iyayen shi (bidiyo)
Majiyar Legit.ng ta ruwaito dansandan yana shaida ma Kotu cewar “Mun cafke Juliet ne yayin da ta shammaci uwar yaron tana kan hanyar tafiya da shi, a lokacin da wata mata ta kwala ihu. Nan da nan jama’a suka farga.”
Sai dai bayan sauraron karar, Alkalin Kotun Ikeja, Taiwo Akanni ya bada belin wanda ake zargi, a kan Naira 100,000, tare da gabatar da shaidu guda biyu, daga karshe kuma ya dage sauraron karar zuwa 31 ga watan janairun shekarar 2018.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng