Labari mai dadi: Jiragen ruwa 28 sun iso tashar jirgin ruwa na Lagas auke da man fetur da kayayyakin abinci
Ana sa ran Jiragen ruwa ashirin da takwas masu dauke man fetur, kayan abinci da sauran kayayyaki zasu sauka a tashoshin jiragen ruwa dake Apapa da Tin Can Island a Legas daga ranar Talata 4 ga watan Janairu, 2018.
Hukumar tashar jirgin ruwa na Najeriya (NPA) ta bayyana a rubutunta, “Shipping Position”, littafin wanda aka bayyanawa manema labarai a Legas a ranar Talata.
Jiragen ruwan suna dauke da alkama, kwantena mara kaya, kifaye, gas da kanwa.
Sauran kayayyaki da jiragen ke dauke da su, a cewar NPA, sun hada da gas, takin zamani, man jirgin sama, man dizal, fetur da kwantena kwantena masu dauke da kaya.
KU KARANTA KUMA: Hukumar NDLEA ta kama matasa 617, ta kuma kwace tan 3.5 na miyagun kwayoyi a jihar Jigawa
Kamfanin dillancin labarai (NAN) ta rahoto cewa jiragen ruwa shida masu dauke da takin zamani, man jirgin sama da man fetur sun sauka a tashar jirgin ruwa a Legas a halin yanzu, suna kuma jiran masauki.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng