Dandalin Kannywood: Adam A. Zango ya sha alwashin kayatar da masoyan sa a sabon fim din Gwaska
Shahararren fim din da aka dade ana jira ya fito na Hausa wanda fitaccen jarumin nan ya fitar mai suna 'Gwaska an shirya fara nuna shi a gidan kallo a ranar 1 ga watan Janairu na shekara mai kamawa ta 2018.
A ranar dai mashiryin shirin da kuma ya taka muhimmiyar rawa a ciki tare da bayar da umurni, Adam A. Zango ya bayyana cewa tabbas fim din zai kayatar sosai domin kuwa sabon fim din mai suna 'The Return of Gwaska' ya banbanta da sauran wadan da suka fita kasuwa a baya.
KU KARANTA: Fitattun jarumai 5 da suka girgiza masana'antar Kannywood a 2017
Legit.ng haka zalika ta samu cewa fitaccen jarumin har ila yau ya kuma bayyana cewa dalilin da yasa har yanzu fim din bai fita ba shine domin a ba dukkan masu ruwa da tsaki a harkar damar kallon fim din tare da yi mashi dukkan gyare-gyaren da suka kamata.
Fitattun yan fim din da suka taka rawa a cikin fim din dai sun hada ne da Adam A. Zango din kansa, sai Bello Muhammad da kuma Lilisco da dai sauran su.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng