Fitattaun jarumai 5 da suka girgiza masana'antar Kannywood a 2017
A dukkan sana'a da ma sauran fannoni na rayuwa za mu samu cewa a kwai wadanda Allah ya yarjemawa suka fice suka zarta sauran daga lokaci-zuwa lokaci.
To haka lamarin yake ma a masana'antar shirya fina-finan Hausa da akeyiwa lakabi da Kannywood inda a kowace shekara akan samu cewa wasu jaruman sukan zarta wasu wajen taka muhimmiyar rawa.
Legit.ng ta yi duba na tsanaki sannan ta zakulo wadanda take ganin kusan a iya cewa shekarar nan ta 2017, ta su ce duba da irin tadda tauraruwar su ta haskaka sosai.
1. Rahma Sadau
Ko shakka babu wannan jarumar ta taka muhimmiyar rawa a masana'antar ta Kannwood duk kuwa da kasancewar ta a matsayin korarriya.
A cikin shekarar ne dai jarumar ta taka rawa a fina-finai kamar haka: "Ajuwaya," "Hakkunde," sai wasu na turanci irin su "Accidental Spy," "Tatu" da kuma EbonyLife har da "Sons of the Caliphate." Haka nan kuma jarumar ta fitar da fim din ta na farko mai suna 'Rariya'.
2. Maryam Yahaya
Jarumar dai da ke matsayin bakuwar fuska ta taka muhimmiyar rawa ne a cikin fim din nan da ya shahara watai 'Mansoor' inda saboda haka ne ma har tauraruwar ta ta fara haskawa sosa.
3. Ali Nuhu
Hakika idan dai ana maganar bango abun jingina ga dukkan masu sana'ar fim din Hausa, to dole ne a fadi sunan Ali Nuhu saboda irin rawar da ya dade yana takawa a masana'antar.
Wasu daga cikin fina-finan da ya yi a 2017 sun hada da: "Ojukokoro," "Banana Island Ghost" da kuma "Hakkunde." Sannan kuma ya shirya fim din 'Mansoor'.
4. Maryam Booth
Ita ma dai wannan jarumar duk da ba'a fiya ganin ta ba a cikin fina-finan da yawa ba a halin yanzu amma ta samu nasara sosai a shekarar 2017.
Wasu daga cikin fina-finan da ta yi sun hada da: "Rariya,""Hakkunde," da kuma "Sons of the Caliphate."
5. Yakubu Mohammad
Shi ma dai wannan jarumin ya taka muhimmiyar rawa a fina-finai da dama a shekarar nan ta 2017 ba ma na Hausa ba kadai har ma da na kudancin kasar nan inda kuma yayi fice sosai.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng