Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Da alama dai fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Hausa a masana'antar Kannywood wadda aka kora a da watau Rahma Sadau ta shirya tarar rigima bayan da tayi fatali da dukkan korar da akayi mata sannan ta shirya sannan ta kuma fito a matsayin jaruma a wani sabon fim mai suna 'Dan Iya.'

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim
Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

KU KARANTA: Aisha Buhari ta ziyarci domin kaddamar da aiki

Fim din dai kamar yadda muka samu daga majiyar mu an shiyar kammala shi sannan a kuma sake shi zuwa kasuwa a watan Maris din shekara mai zuwa ta 2018 sannan kuma fitaccen mai bayar da umurnin nan watau Yaseen Auwal ne ya bayar da umurnin fim din.

Legit.ng dai ta samu cewa fim din na barkwanci ne kuma an shirya shi a wani kauye ne da yake nuna rayuwar manyan jarumai Rahma Sadau da kuma Sadiq Sani Sadiq wanda shine ya fito a matsayin dan iya din.

Sauran wadanda suka taka rawa a shirin fim din sun hada da Rabi'u Rikadawa, da kuma Aminu Sheriff Momoh.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a ranar 3 ga watan Oktobar bara ne dai kungiyar masu shirya-fina-finan Hausa shiyyar jihar Kano ta dakatar da jarumar sakamakon wata waka da tayi da ta sabawa addini da kuma al'adar mutane.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng