Inna Lillahi wa inna Ilaihi raji’un: Allah ya yi ma Sule Katagum, Wazirin Katagum 95, rasuwa
-Wazirin masarautar Katagum, Alhaji Sule Katagum ya rasu
- Sule Katagum ya rasu ne kwanaki kadan bayan rasuwar Sarkin Katagum
A daren Lahadi 17 ga watan disamba ne Allah yayi ma wazirin Katagum, Alhaji Sule Katagum mai shekaru 95 bayan fama da doguwar rashin lafiya, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.
Rashin lafiyar Sule Katagum ta yi tsanani ne tun bayan rasuwar amininsa, mai martaba Sarkin Katagum Alhaji Muhammadu Kabir Umar a satin data gabata, kuma ya rasu ya bar iyalai da dama.
KU KARANTA: Gurgu ka fi mai ƙafa iya shege: An kama wani gawurtaccen ɗan fashi mai ƙafa ɗaya (Hotuna)
Daga cikin yaran sa akwai Hajiya Mairo S Katagum Audu Sule Katagum, shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar Bauchi, Alhaji Ahmadu S Katagum, Hajiya Fati S Katagum, Alhaji Abu S Katagum, da dai sauransu.
Marigayi Sule ya ya taba zama shugaban ma’aikatan Najeriya daga shekara 1963 zuwa 1975.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng