Kazamin rikici na cigaba da wanzuwa tsakanin Dangote da Bua kan wurin hakar ma'adinai
- Rikici ya barke tsakanin manyan masu kudin Arewa
- Hamshakan masu kudin dai sune Dangote da kuma BUA
- Rikicin nasu duk saboda wajen hakar ma'adanai ne
Da alama dai babu alamun kaiwa karshen rikicin dake tsakanin hamshakan masu kudin nan na Arewa 'yan asalin garin Kano watau Alhaji Aliko Dangote shugaban rukunin kamfunnnan Dangote da kuma Dan Alhaji Isiaka Rabi'u shugaban kamfunan BUA kan lasisin wani wurin hakar ma'adanai mai lamba 2541 a garin Okene na jihar Kogi.
KU KARANTA: Wasu bakin haure sun zautu saboda ukuba a Libiya
Mun samu dai cewa yayin da mahukuntan kamfanin na Dangote ke zargin kamfanin BUA da hakar ma'adanai a wurin da ba nasu ba, su kuma shugabannin na BUA zargin Dangote suke yi da hada baki da gwamnatin tarayya wajen ganin sun kwace masu wurin mai tarin albarka.
Legit.ng dai ta samu cewa babban Darekta na kamfanin Dangote mai suna Devakumar Edwin ya nuna rashin jin dadin sa game da yadda 'yan kamfanin na BUA tuni suka fara shiga kafafen yada labarai suna bata masu suna game da lamarin tun kafin kotun gwamnatin tarayya ta yanke hukunci.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng