Zakir Naik ya shiga halin o ni ‘yasu

Zakir Naik ya shiga halin o ni ‘yasu

- Gwanatin kasar indiya ta dau alwashin garkame Dakta Zakir Naik

- Hukumomin Indiya sun rufe tashar talabijin din sa mai sunna Peace TV

- Indiya ta na zargin Zakir Naik da daukan nauyin yan ta'adda

Gwamnatin Indiya ta dau alwashin garkame shahararren malamin addninin muslunci na duniya dakta Zakir Naik.

A watannin da suka gabata ne shugabannin indiya suka kai karar Zakir Naik gaban hukumar yansanda na kasa da kasa wato (Interpol) suna neman aka kama shi.

Amma hukumar Interpol ta yi watsi da karar saboda basu da kwararan dilalai akan sa.

Zakir Naik ya shiga halin o ni ‘yasu
Zakir Naik ya shiga halin o ni ‘yasu

A wannan karon ne gwamnatin Indiya ta kara kai karar Zakir Naik wajen yansanda bisa zargin zama ummul’abisar harin da yan ta’adda suka kai babban birnin Dhakka dake kasar Bangladesh.

KU KARANTA : Ike Ekweremadu ya bayyana abin da ya sa ake neman fetur a Arewacin Najeriya

Wannan ya janyo aka kwace fasfot din sa a watan Yuli da ya gabata.

Dr Zakir Naik babban mallamin addinin musulunci ne da ya shahara wajen muhawara da masuyar yawu a fannoni daban-daban na addinin musulunci.

Hukumomin Indiya sun rufe tashar talabijin din sa mai sunna Peace TV wanda ke da farin jini sosai.

Dr. Zakir Naik yana da miliyoyin masoya a fadin duniya kuma ya jagoranci tarukan addinin musulunci da ya kai dubu 4.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng