'Yan dabar Kaduna sunyi 'shara' a titunan Kaduna dazu da yamma
- Rashin aikin yin samari da matsalolin shaye-shaye sun sa samari sare-sare
- Sunyi rashin mutuncin ne bayan da suka sami taron jama'a da suke dawowa daga hawan durbar
- Sun kwaci wayoyi da sarar mutane.
Rashin aikin yi da shaye-shaye na samari a Kaduna ya sanya samari sun lalace. Wasu 'yan daba da ake kira 'yan shara sun fito da yawansu da muggan magamai suna yi wa mutane fashi da makami.
A wannan yammaci dai, sun kwaci wayoyi da sarar mutane da basu ci ba basu sha ba. Kowa yana ta gudu, a unguwar Badawa da Malali.
DUBA WANNAN: Buhari zai cika shekaru 75 a duniya
An dai kirawo 'yansanda inda suka zo suka kwantar da rikicin, sun kuma yi shara suma, inda suka nade da yawa daga cikin masu aika-aikar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng