Dandalin Kannywood: Zan so diyar ciki na tayi harkar fim - Sadiq Ahmad

Dandalin Kannywood: Zan so diyar ciki na tayi harkar fim - Sadiq Ahmad

Jarumin nan na fina-finan Hausa a masa'antar Kannywood mai suna Sadiq Ahmad ya bayyana cewa shi zai so diyar sa ta yi harkar fim don bai ga wani abu ba a cikin ta.

Jarumin ya bayyana haka ne a yayin da yayi wata fira da majiyar mu dake wallafa mujallar da ta jibanci harkar fim a watannin baya.

Legit.ng ta samu cewa jarumin yayi wannan bayanin ne a lokacin da yake ansa wata tambaya da aka yi masa game da ko zai iya barin diyar sa ta cikin sa tayi harkar fim.

Dandalin Kannywood: Zan so diyar ciki na tayi harkar fim - Sadiq Ahmad
Dandalin Kannywood: Zan so diyar ciki na tayi harkar fim - Sadiq Ahmad

KU KARANTA: DPR ta hukunta gidajen mai 10 bisa laifin tsadar mai

A ansar da jarumin ya bayar kuwa ya bayyana cewa tabbas zai iya barin ta domin kwa ba wani abu bane.

"E, zan iya barin ta ta yi. Ai ba wani abu bane," in ji shi.

Sai dai kuma ya bayyana cewa ba zai tursasa mata ba wajen cewa dole sai ta yi fim din ba inda yace duk abun da take so shine za ta yi.

A cewar sa: " Kasan bahaushe yace ka haifi mutum, baka haifi halin sa ba; za ta iya yiwuwa na ce tayi amma ita kuma tace burin ta ta zama lauya ko likita, kaga kenan babu yadda zan yi da ita."

dan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng