'Dan Sarki Sanusi II ya zama dan-doka kamar Kakansa
- Sarki Ado Bayero ma yayi wakilin doka a lokacin baya
- Marigayi Ado Bayero kawu ne ga Sarki Sunusi na yanzu
- Saurayin 'da ne ga sarkin Kano Muhammadu Sunusi II
Sarkin Kano Sunusi Lamido ya baiwa Najeriya dansa, Yarima Aminu domin hidimtawa tsaro, a bikin saukar daliban da aka yi a makarantar horaswa a jihar Pulato a bana, a yau dinnan.
Saurayin dai, Mal. Aminu, ya fara da igiya 2 a matakin farko na bauta ma kasa ta fannin 'yansanda, aiki da Kakansa ya taba yi kafin ya zamo sarki a Kano, lokacin mulkin turawa.
DUBA WANNAN: Iran na fuskantar barazana daga Amurka
An ga Sarkin na Kano tare da iyalansa suna biki da murna, tare da Allah sanya alheri, a wurin saukar. Sarki Ado yana saurayi yayi 'dan doka watau kamar dai dan-sandan zamani
Muna musu fatan ayi a gama lafiya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng