Limamin masallacin makka ya soki masarautar kasar bisa maido da gidajen Sinima
Labaran da muke samu dai na nuni da cewa watan Janairun babban Limamin Masallatan makka na Harami mai suna Sheikh Abdul-Aziz ashSheikh yayi Allah-wadai tare da gargadi ga masarautar Saudiyya game da illolin gidajen sinima, yana mai cewa za su bata tarbiyyar yan kasar.
Wannan dai ya biyo bayan wani kuduri da Yariman masarautar mai jiran gado ya fitar inda ya bayyana cewa kasar ta dage haramcin gina gidajen Sinima din sannan kuma zata fara bayar da Lasisi ga dukkan masu bukata daga watan Janairu mai kamawa na shekrar 2018.
Legit.ng dai ta samu cewa gidan sarautar na Saudiyya da kuma shi kansa Limamin masalacin suna bin mazahabin Sunnah ne.
Haka ma dai wasu mawakan gambara na turanci watau hip hop irin su Nelly da Ceb Khaled za su yi waka a birnin Jedda ranar Alhamis, ko da yake maza ne kawai za su halarci wurin.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng