Bincike ya nuna musulmai 6,000 aka yi ma kisan gilla a kasar Myanmar
Bayan tattara bayanai daban daban, kungiyoyin kare hakkin dan adama da ma jami’an majalisar dinkin duniya sun tabbatar da yawan musulman da aka kashe a kasa Burma sun kai dubu shidda.
BBC Hausa ta ruwaito wannan alkalumma da aka fitar ya samu ne bayan tambayoyi da kungiyoyin suka yi da yan gudun hijira musulmai dake zaune a sansanin yan gudun hijira a kasar Bangladesh.
KU KARANTA: Alheri gadon barci: Halayyar kirki da wani mutumi ya nuna ma wata Zakanya ya sa sun shaƙu da juna
Dukkanin jama’an an kashe su ne bayan da rikici ya balle a jihar Rakhine, in da mayakan sa kai yan Rohinja, har ma da Sojojin kasar suka dinga kai ma Musulman Rohingya a watan Agustan 2017.
Wata kungiyar likitoci masu bada agaji, mai suna ‘Medicine San Frontiers’ ta gudanar da bincike a sansanin yan gudun hijira, inda tayi magana da mutane 2,500, inda ta gano a baya ba’a ruwaito asalin adadin mutanen da suka mutu ba, suka ce adadin wadanda suka mutu sun wuce wanda aka sanar.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito kungiyar ta na kiran da dama daga cikin mutanen sun mutu ne sakamakon harbin bindiga, ko kuma ciwuka da suka samu daga harbin, da haka ne ake kira ga majalisar dinkin duniya a kan ta gudanar da bincike don tabbatar da gaskiyar da lamarin tare da hukunta masu laifi.
Sai dai tuni rundunar Sojojin Myanmar ta wanke jami’an Sojojn ta daga aikata wani laifi dangane da kisan kiyashin da suka yi ma Musulmai.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng