Ku sadu da Baba Umar Farouq, wanda ake tsammanin ya maye gurbin Sarkin Katagum

Ku sadu da Baba Umar Farouq, wanda ake tsammanin ya maye gurbin Sarkin Katagum

Tun bayan mutuwar Sarkin Katagum Alhaji Kabir Umar ake ta rade-raden cewa Sarkin na gaba da zai gaje shi zai fito ne daga cikin 'ya'yan da ya haifa inda kuma masu sharhi suka fi ganin babban dan nasa ne zai maye gurbin na sa kamar dai yadda tarihi ya tabbatar.

Haka nan kuma babban dan na marigayi Sarkin shine Alhaji Baba Umar Farouq kamar dai yadda binciken mu ya tabbatar dake zaman yaya ga dukkan 'ya'yan 48 da Sarkin ya bari a duniya yayin rasuwar sa da shekara 89.

Ku sadu da Baba Umar Farouq, wanda ake tsammanin ya maye gurbin Sarkin Katagum
Ku sadu da Baba Umar Farouq, wanda ake tsammanin ya maye gurbin Sarkin Katagum

Legit.ng dai ta samu cewa Alhaji Baba Umar dai na zaman tsohon babban Sakataren din-din-din na gwamnatin tarayya sanna kuma yanzu haka shine Hakimin Shira duk dai a gundumar masarautar ta Katagum.

Sai dai da majiyar mu ta tuntubi masu ruwa da tsaki a harkar masarautar, sun bayyana cewa ko tantama babu cewar babban dan na sa ne zai maye gurbin sa don kuwa har ma sauran 'ya'yan da Sarkin ya bari tuni har sunyi mubayi'a.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng