Dalilin da yasa gwamnati ta kaura da babban birnin Najeriya daga Legas zuwa Abuja – Inji Gowon
- Yakubu Gowon ya bayyana dalilin da ya sa gwamnati ta kaura da birnin tarayya daga Legas zuwa Abuja
- Gowon ya ce gwamnatinsa ne ta yi shawara na kawar da birnin tarayya daga Legas zuwa Abuja
- Tsohon shugaban ya ce shawarar kaura zuwa Abuja ta dogara ne a kan tsaron yankunan kasar
Tsohon shugaban kasa, Janar Yakubu Gowon (mai ritaya), ya bayyana cewa kawar da babban birnin Najeriya daga Legas zuwa Abuja ya dogara ne kan yancin yankunan ƙasar.
Kamar yadda Legit.ng ke da labari, Gowon ya bayyana hakan ne a bikin ranar tunawa da aka kaura da fadar gwamnatin tarayya daga Legas zuwa Abuja ranar Talata, Disamba 12 a Abuja.
Ya ce shawarar kaura zuwa Abuja ta dogara ne a kan tsaron yankunan kasar.
"Na zagaye don ganin sauran manyan biranen tarayya na ƙasashen duniya kuma muna buƙatar wani wuri wanda ya kasance tsakiya don kawar da cinkoson Legas, a lokacin ne muka yi tunanin wannan shirin, amma zai aka samu canjin gwamnati", in ji shi.
KU KARANTA: Ba za mu koma PDP ba don mu ba yaran Atiku ba ne Inji Kwamishinonin Adamawa
Tsohon shugaban ya yaba da ci gaba da shirin wanda aka yanke shawara a kai a shekara ta 1974, amma a shekara ta 1976 amma cimma burin, ya kara da cewa jihar Legas za ta ci gaba da zama mafi karfi na tattalin arzikin kasar.
A jawabinsa, ministan birnin tarayya, Malam Muhammad Bello, ya ce wannan bikin wata dama ce don sake nazari a kan kaura da fadar gwamnati a shekaru 26 da suka gabata.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng