Rashin bin doka ke janyo rikici tsakanin manoma da makiyaya a Najeriya
- Gwamnatin tarayya ta fito da tsarin da zai kawo karshen rikicin makiyaya da manoma
- Mataimakin shugaban kasa ya gana da Sarakuan Arewa akan matsalar rikicin makiyaya da manoma da makiyaya a Najeriya
Gwamnatin Najeriya ta fito da sabuwar tsarin da zai kawo karshen rikicin da yake yawan barkewa tsakanin makiyayan Fulani da manoma a Kasar.
A makon da ta gabata ne mataimakin shugaban kasa Ferfesa Yemi Osinbajo ya tattauna da masu ruwa da tsaki a kasar da samun mafita daga matsalar.
Mataimakin shugaba kasa ya gana da mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na II, Lamidon Adamawa, Muhammadu Barkindo Aliyu da dakta Aliyu Tilde tare da wasu shugabannin Fulani akan matsalolin makiyaya da manoma.
Bayan sun kammala taron Dakta Aliyu Tilde ya fadawa yan jarida cewa, sun fito baro-baro sun fadawa mataimakin shugaban kasa irin matsalolin da makiyaya ke fuskanta a kasar.
KU KARANTA : Yara dubu 170 ke hawa yanar gizo a kullum - UNICEF ta yi gargadi
A makon da ya gabata ne mataimakin shugaban kasar Najeriyar, Farfesa Yemi Osinbajo, ya ziyarci garin Numan na jihar Adamawa bayan rikici dake kabilanci ya barke tsakanin Fulani da yan kabilat Bachama.
Rikicin yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama wanda ya kunshi kananan yara da mata.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng