Ku taimaka mani: Wata kwarkwarar marigayi Ado Bayero ta yi kukan ukubar talauci
Wata daya daga cikin kwarkwarorin da marigayi sarkin Kano Ado Bayero ya bari a duniya mai suna Hauwa Momoh ta koka akan yadda talauci yanzu yayi mata katutu tun bayan mutuwar mijin nata shekarun baya da suka shude.
Hajiya Hauwa wadda take da shekaru akalli 51 a duniya dai a yayin da take zantawa da manema labarai ma dai ta bayyana yadda take fama da zazzabi amma maganin ma wani ne ya sai mata shi.
KU KARANTA: Tibubu ya fada a matsala da gwamnonin APC
Legit.ng dai ta samu cewa ita Hajiya Hauwa diya ce ga marigayi Sarkin Auchi dake jihar Edo mai suna Ahmed Momoh da kuma ke zaman aboki ga Sarkin na Kado Ado Bayero kafin rasuwar sa.
A cewar ta mahaifinta ne dai ya baiwa Sarkin na Kano amanar ta a shekarun baya inda shi kuma Sarkin ya mayar da ita kwarkwarsa ya kuma ajiye ta a unguwar Gandun Albasa inda ya cigaba da kula da ita tamkar matasar kafin rasuwar tasa.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng