Kafa Tarihi: Yarinya 'yar shekara 14 ta zama gwamnan jihar Abia na awa 24
Gwamnan jihar Abia dake a kudu maso gabashin Najeriya, Okezie Ikpeazu a jiya Litinin ya bar tarihi a inda ya nada wata yarinya mai shekaru 14 kacal a duniya mai suna Joy Ezechikamnayo a matsayin Gwamnan jihar na tsawon kwana daya.
Ita dai yarinyar wadda ita ce shugabar daliban makarantar Intellectual Giants Christians Academy a garin Umuahia ta zamo gwarzuwar shekara ne bayan da ta yi kwazo sosai a yayin kammala wata gasar rubutun hikaya a satin da ya gabata.
KU KARANTA: Za mu gama da Boko Haram kwanan nan
Legit.ng ta samu cewa ita dai yarinyar Joy Ezechikamnayo gwamnan ya yassare mata ne ta zama gwamnar jihar ta kuma zartar da dukkan abunda ta ga ya dace tare da sauran 'yan majalisun zartarwar ta da aka samo mata.
A yayin zaman nata a matsayin Gwamna, Joy Ezechikamnayo wadda aka haifa a ranar 18 ga watan Maris din shekarar 2003, ta dauki matakin sanar da dukkan ranar 12 ga watan Disemba a matsayin ranar yara a jihar.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng