Neman Duniya: Wani dan siyasa ya jefa jinjiri a rijiya saboda neman cin zabe

Neman Duniya: Wani dan siyasa ya jefa jinjiri a rijiya saboda neman cin zabe

- Wani dan takarar majalisar wakilai a jihar Taraba ya jefa jariri a cikin rijiya

- Dan siyasar tare da ‘yan uwansa suka aikata wannan ta’asa

- Bayan jefa wannan jinjiri rijiya nan da nan Allah ya tona musu asiri, take aka kama daya daga cikinsu

Wani dan takaran neman kujerar majalisar wakilai na Jalingo , jihar Taraba, Yorro Zing ya sanya jinjiri tare da sihiri a cikin rijiya, a Unguwar Sintali da ke Jalingo, babban birnin jihar.

A yammacin ranar juma’a, 8 ga watan Disamba ne dan takaran majalisan ya turo ‘yan uwansa na jini da kuma wasu matasa a Unguwar Sintali wanda suka yi wa tawagar zuwa wani gida kusa da gidan Alhaji Ali Jillari domin gidan yana da wata tsohuwar rijiya wanda aka juma ba’a amfani da ita.

Majiyar Legit.ng ta tabbatar da cewar, a wannan rijiyan ne suka jefa jaririn a hade da sihiri, nan da nan bayan jefa wannan jinjiri sai Allah ya tona musu asiri, nan take aka kama daya daga cikinsu aka kai ofis na sibil difens reshen jihar Taraba, inda aka masa tambaya menene suka jefa a rijiyar, sai ya ce wai dibino ne guda bakwai aka ce su jefa a rijiyar, nan take ne mutanen gidan suka yi tir cewa basu yarda ba sai dai a yashe rijiyan.

Neman Duniya: Wani dan siyasa ya jefa jinjiri a rijiya saboda neman cin zabe
Yayin yashe rijiyar da aka jefa jaririn

KU KARANTA: Ba a haifi wanda zai iya kada Buhari zabe ba 2019 - Inji wani jigon APC

A safiyar ranar Lahadi aka zo yashe rijiyan tare da tawagar dan takaran majalisan, nan aka fitar da wani bakin leda da wani abu a cikin ta, take wani daga cikin tawagar ya sundumi ledan suka ruga aguje, matasa sukayi ca akansu suka musu duka suka kwace ledan, yayin bude ledan sai ga jariri da wasu abubuwa a jikinshi.

Neman Duniya: Wani dan siyasa ya jefa jinjiri a rijiya saboda neman cin zabe
Rijiyar da aka jefa jinjiri a Unguwar Sintali

Take matasa suka rufesu da duka sai da ‘yan sanda suka kwacesu a hannun matasan.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng